Yau dai mako guda kenan da rufe filin jiragen na babban birnin tarayya domin yi masa gyara. A cewar Injiniya Saleh Dinoma, shugaban hukumar filayen saman Najeriya, yanzu haka ana nan ana gudanar da aiki a tashar jiragen.
Wakilin Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, ya ziyarci filin saukar jiragen na Abuja domin ganin yadda aiki yake wakana, inda yace yaga manyan motocin da ke gudanar da aikin wasu na banbare hanyar da jirgi yake sauka domin maye gurbinta da sabuwa.
To sai dai masu hada-hadar kasuwanci a filin jiragen saman na Abuja, na kokawa game da wani hali da suka shiga na rashin ciniki, wadanda yanzu haka ke fatan za a kammala wannan aiki cikin wa’adin da aka shata.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum