Kwararowar Hamada Da Boko Haram Suna Barazana Ga Kasar Kamaru Da Makwabta

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya

Miliyoyin mutane na fuskantar barazanar yunwa a kasar Kamaru da yankunan dake makwabta sakamakon kwararowar hamada da kuma hare haren kungiyar Boko Haram

Gwamnatin kasar Kamaru tace yankin kan iyakarta da Najeriya, da Chadi, da kuma galibin yankin tafkin Chadi yana fuskantar matsalar karancin abinci sabili da kwararowar hamada, da kuma tashin hankalin kungiyar Boko Haram da ya hana manoma gudanar da ayyukansu.

Hukumomi sunce kwararowar hamada ya shafi kashi arba'in cikin dari na kan iyakar kasar da Najeriya da kuma Chadi, kuma zai iya haifar da yunwa da zata shafi kashi talatin cikin dari na mutane miliyan uku dake zaune a yankin na arewacin kasar, da ya hada da 'yan gudun hijira daga Najeriya dubu tamanin da kuma 'yan gudun hijira na cikin gida dubu dari.

Kasar dake tsakiyar Afrika tace lamarin zai iya kara muni sabili da tashin hankalin kungiyar Boko Haram ya hana manoma aiki a gonakinsu, abinda ya sa abincin da ake nomawa ya ragu ainun.

Lamarin ya kuma yi muni a kasashen dake yankin Chadi wadanda ke dogara ga kasar Kamaru domin samun abinci yayinda ake fama da hare haren mayakan.