Manyan hafsoshin soja daga Kamaru da Najeriya sun zauna suka yi shawarwari cikin sirri a Maiduguri, kan irin matakan hadin guiwa da zasu dauka domin kawo karshen ayyukan 'yan Boko Haram a cikin kasashensu.
A bayan wannan ganawar da suka yi, Birgediya-janar Frederick Jonket na rundunar sojojin Kamaru yace su na hada kai sosai da sojojin Najeriya, musamman wadanda suke karkashin shir5in yaki da Boko Haram na Operation Lafiya Dole, domin fatattakar 'yan ta'adda daga wannan yanki.
Yace duk da irin matsalar kayan aiki da ake fuskanta a wasu lokuta, sassan su kan hada kai su samar da abubuwan da ake bukata domin yakar 'yan Boko Haram.
Babbamn kwamandan Opertation Lafiya Dole, Manjo janar Rogers Nicholas, yace babban abinda ya kawo tawagar sojojin na Kamaru zuwa Najeriya shine auna irin matakan da za a iya dauka, "na hana 'yan Boko Haram shiga Kamaru daga Najeriya, ko kuma shigowa Najeriya daga Kamaru."
Yace a yanzu haka sassan biyu su na hada kai a irin fatattakar da ake yi ma 'yan Boko Haram daga Sambisa, kuma da zarar sun samu galaba a wannan yanki, zasu maida hankulansu kan tsaunukan Mandara, wadanda suka shiga har cikin Kamaru, inda kuma 'yan Boko Haram din ke buya.
Manajo janar Nicholas ya ce, "a yanzu haka yaranmu da kayan aikinmu, da yaransu (Kamaru) da kayan aikinsu, da kuma musanyar bayanai na leken asiri duk muna yi tare da su. Kuma hakan yana kawo amfani."
Ga cikakken bayani a wannan rahoto na Haruna Dauda daga Maiduguri
Facebook Forum