Su dai ‘yan awaren na Ambazoniya na kudancin kasar Kamaru, na fafutukar kafa kasar su ne batun da ya kai su fito na fito da kuma yakin sari-ka-noke da mahukuntan kasar, wanda a kan samu asarar rayuka a wasu lokutan.
Kamar yadda mazauna yankunan kan iyaka suka tabbatar, a kan samu bullarsu a wasu yankuna na jihar Taraba dake makwabtaka da kasar Kamaru. Kuma don ganin an sa ido, game da kwararar ‘yan awaren da kuma batutuwan tsaro ne yasa gwamnatin jihar kiran taron sirri na tsaro da sarakunan jihar musamman wadanda suka fito a yankunan kan iyakan, taron da mataimakin gwamnan jihar Haruna Manu ya jagoranta.
Mataimakin gwamnan ya ce dole a tashi tsaye game da batun shigowar ‘yan awaren na Ambazoniya. a cikin jawabinsa ya bayyana cewa, “Suna shigowa ne ta ruwa da kuma barauniyar hanya, don haka muke kira ga gwamnatin tarayya da ta dau mataki wajen jibge sojin ruwa da sauran jami’an tsaro”.
Da yake karin haske, mataimakin gwamnan ya ce baya ga batun ‘yan awaren na Ambazoniya, haka nan kuma aka tabo batutuwan da suka shafi rikicin makiyaya da manoma da kuma batun sababbin masarautun da aka kirkiro.
Tun farko a jawabin sa, gwamnan jihar Taraban Akitet Darius Dickson Isiyaku ya ce don kara inganta harkar tsaro, gwamnatin jihar zata hada kai da sarakuna iyayen al’umma, musamman a wannan lokaci da gwamnatin tarayya ke marawa shirin sintirin al’umma, wato “community policing” baya, inda ya ce zasu yi amfani da zaratan ‘yan mashal don kwalliya ta biya kudin sabulu.
Ko a kwanaki baya sai da jami’an tsaro suka samu cafke wasu ‘yan awaren na Ambazoniya bisa zargin cewa sun shigo Najeriya ta yankin karamar hukumar Sardauna, domin sayen makamai.
Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz cikin sauti
Your browser doesn’t support HTML5