Kwana 56 Mu Ka Yi Mu Na Kange Dandalin Unity Daga 'Yan Peter Obi- 'Yan Gani Kashenin Tinubu

Gani Kashenin Tinubu

Wasu 'yan kungiyar gani-kashenin zabebben shugaban Najeriya Bola Tinubu su ce sun cika kwanaki 56 su na kange dandalin UNITY daga magoya bayan dan takarar jam'iyyar Leba Peter Obi.

Dandalin dai shi ne mafi girman wajen yin gangami ko zanga-zanga a tsakiyar babban birnin Najeriya Abuja inda magoya bayan Tinubun ke zaman dirsham don hana 'yan adawa kutsowa cikinsa.

Masu zaman dirshan din kan yi rawa da waka har ma da tara yara kanana a na ruwaito mu su tatsuniyoyin gizo da koki don fagen ya zama da sha'awa har tsawon kwanakin da yanzu za su gama zaman ranar rantsar da Tinubu a 29 ga watan nan.

Gani Kashenin Tinubu

Gabanin fara zaman na su, 'yan Leba kan zo dandalin don yin watsi da ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben 25 ga Febreru inda wasu kuma kungiyoyin ke kiran kafa gwamnatin rikwan kwarya don shirya sabon zabe.

Gani Kashenin Tinubu

Daya daga cikin su, Auwal Bashir ya ce hankalin su na kwance don gudunmawar da su kan ba wa kan su ko goyon baya daga wani jigo a tafiyar Tinubu.

A martanin sa kakakin kamfen din Obi da Datti Dr.Yunusa Tanko ya ce ba ya shakkar masu zaman dirshan din don su ma kullum sai sun yi gangami amma a kan titunan Abuja ba bugewa a waje daya ba.

Abuja ta fara daukar haramar rantsar da Tinubu inda akasarin 'yan siyasa su ka fi garzayawa masaukin Tinubun maimakon fadar Aso Rock wajen shugaba Buhari da ke shirin ficewa zuwa inda ya fito.

Saurari rahoton Nasiru Elhikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Kwana 56 Mu Ka Yi Mu Na Kange Dandalin Unity Daga 'Yan Peter Obi- Gani Kashenin Tinubu