Kwamitin tsaron kan iyakokin kasashen Kamaru da Najeriya na ci gaba da taro a birnin Yaounde. Kwamitin ya shiga kwana na biyu da fara tattaunawar ta kwanaki uku.
Kwamitin tsaron kan iyakokin kasashen biyu na yin taron ne da nufin wanzar da zaman lafiya a kan iyakokin su, da kuma kawo karshen tashe-tashen hankulan da 'yan kungiyar Boko Haram ke haddasawa akai-akai.
Karo na uku kenan da kwamitin kan iyakokin Kamaru da Najeriya ke shirya irin wannan taro.
A ranakun takwas zuwa goma sha daya ga watan yulin shekarar da ta gabata ta dubu biyu da goma sha hudu kwamitin yayi taron shi na biyu a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Wakilin Sashen Hausa a kasar Kamaru Mamadou Danda ya aiko karin bayani akan taron kamar haka:
Your browser doesn’t support HTML5