Kwamitin ya gudanar da ayyukan samar da lafiya da suka hada da yin aikin tiyatar a idanu da ta makogwaro da dai sauran wasu cututtuka.
Shirin ya tallafawa kimanin mutane maza da mata 15,000 da suka amfana daga shirin ayyukan, kuma kyauta.
An gudanar da irin wadannan ayyuka a jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Yobe da kuma Gombe.
Aikin da kwamitin ya gudanar da jihar Gombe, al’ummar yankunan kananan hukumomi 11 da ke jihar da ma wasu da suka fito daga jihohin da ke makwabtaka duk sun amfana daga wannan shiri.
A cewar jagoran shirin a Gombe kuma sakataren kwamitin, Alhaji Tijjani Tumsa, suna da likitoci kimanin 100 yanzu haka a Gombe da suke ba da tallafin kiwon lafiya.
Muryar Amurka ta samu zantawa da wasu mutanen da suka sami cin moriyar wannan shiri, wadanda suka bayyana jin dadinsu ganin cewa sun dade suna fama da cututtuka amma saboda rashin kudi sun kasa zuwa asibiti.
Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Mohmmad.
Your browser doesn’t support HTML5