Kwamitin sulhu na MDD yayi tur da harin da aka kain sojojinta da suke aikin kiyayen zaman lafiya har biyu suka mutu a Mali
WASHINGTON, DC —
Kwamitin sulhu na MDD yayi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai da wata mota, wanda ya kashe sojojin kiyaye zaman lafiya su biyu na MDD a Mali, da kuma jikkata wasu.
Sojojin da harin ya rusa da su daga kasar Senegal suke karkashin shirin kiyaye zaman lafiya na majalisar mai lakabin MINUSMA, lamarin da ya auku a harin na jiya Asabar lokacinda maharin ya tada nakiyoyi cikin motar da yake ciki a harabar bankin da sojojin suke gadi a Kidal.
Haka ma wasu sojojin Mali suna daga cikin wadanda suka jikkata. Babu wanda ya fito nan da nan ya dauki alhakin kai harin.
Kungiyoyin mayakan sakai masu yawa ciki har ta ‘yan awaren abzinawa, sun yi amfani da rudanin da juyin mulkin da sojojin kasar suka ayyana a babban birnin kasar Bamako cikin watan Maris na bara, su kuma suka ayyana iko kan arewacin kasar, inda suka so kafa tsarin tafsarkin shari’a.
Gwamnatin kasar ta sake maida ikonta kan arewacin kasar, bayan matakin soja da kasar Faransa ta kaddamar cikin watan janairun.
Mayakan sakan basu da sauran karfin kadamar da gagarumin matakin soja, amma ‘yan burbudinsu da suka rage suna kai kananan hare hare a arewacin kasar.