Shugaba Muhammadu Buhari ne ya kafa kwamitin binciken karkashin jagorancin Baba Gana Kingibe don gano badakalar kudin da ta jefa hukumar ta NIA cikin matsalar. To yay a karbi rahoton kwamitin.
Idan ba a manta ba dai an bankado makudan kudaden ne da suka kai kimanin Dalar Amurka miliyan arba’in da takwas a gidan tsohon shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya wato National Intelligence Agency a Turance Jakada Ayo Oke da ke unguwar Osborn Towers a Legas.
Bayan kujuba kujubar gano tushen kudaden ne, abubuwa suka dame tsakanin hukumar ta NIA da ta yaki da almundahana da dukiyar kasa wato EFCC, inda a karshe dai aka kafa kwamitin don yin cikakken bincike.
Malam Garba Shehu shine kakakin Shugaba Buhari, yana daya daga cikin wadanda suka halarci taron mika wannan rahoton na kwamitin Jakada Baba Ghana Kingibe. Wannan ce ta sa Muryar Amurka ta tattauna da shi don jin yadda lamarin yake.
Ga rahoton wakilinmu daga fadar Gwamnatin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5