Shawarar kafa kwamitin kare wuraren ibada yayin tashin hankali ta kaiga Najeriya kafa kwamitin da yayi taronsa a Abuja.
Kwamitin na Najeriya yayi taron kwanaki biyu wanda ya samu halartar mutane daga sassan kasar. Malam Tukur Baba Dan Iyan Mutum Biyu kuma malami a jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto yana cikin mahalartan taron.
Malam Baba yace makasudin taron shi ne su yi nazari akan wata kasida da ta ba al'ummomi damar kare wuraren ibadansu a duk lokacin da aka samu rikici da tarzoma. Ana son kowane wurin addini ba'a lalatashi ba ko kuma an ci zarafinsa ba domin cin zarafin wasu koda menene addininsu. Ana son wuraren addini su kasance wurare ne na kare juna.
Wasu da suka halarci taron sun yi tsokaci. Wani Elder Timothy Mshelia da ya fito daga Borno yace yana son addinai biyun nan masu karfi a kasar, wato Musulunci da Kiristanci su rungumi junasu su mayarda wuraren ibada tamkar wuraren zumunci ne. Yace idan Kirista yace musulmi bashi da addini bai yi imani ba. Haka idan Musulmi yace Kirista arne ne to shi ma bai yi imani ba.
Shi ma wakilin Jama'atul Nasril Islam daga Kaduna Muhammadu Raji yace dama can matsayinsu shi ne a samu hadin kai kuma idan babu shi babu cigaban kasa.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5