Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Martaba Sarkin Musulmi Ya Cika Shekaru Goma Kan Karagar Mulki


Sarkin Musulmi Mai Martaba Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III, Sokoto Najeriya
Sarkin Musulmi Mai Martaba Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III, Sokoto Najeriya

An fara bikin cika shekaru goma da Sarkin Musulmi Mai Martaba Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III ya dare kan karagar mulki a Sokoto.

Jiya aka fara bukuwan a birnin Sokoto tare da yin addu'o'i na samun zaman lafiya da cigaban kasar Najeriya tare kuma da neman sauki daga cikin mawuyacin halin da 'yan kasar ke ciki.

Bayan kammala addu'o'in a karkashin sarkin Kano Muhammad Sanusi II jawaban da suka biyo bayan addu'o'in tamkar martani ne ga wasu dake kushin taron binkin cewa ya zo daidai lokacin da 'yan Najeriya ke fama da kuncin rayuwa da kuma mutuwar dimbin mutane a Sokoto sanadiyar barkewar cutar zazzabin cizon sauro.

Sultan Sa'ad Abubakar III yace bikin na yiwa Allah godiya ne akan matsayin da Allah ya dorashi. Yace taro ne na godiya ba na nishadi ba saboda a matsayinsu na musulmai sun kara haduwa, sun kara hada kai domin godewa Allah.

Shi ma gwamnan jihar Sokoto Waziri Aminu Tambuwal cewa yayi sun shirya taron bukukuwan ne ba tare da nema ko yawun sarkin musulmin ba. Yace mai girma sarkin musulmi "bai bukata ba haka kuma bai nema ba". Gwamnan ya cigaba da cewa shugabannin ne a karkashin sarkin Kano Muhammad Sanusi II suka ga ya dace a yi bikin. Yace suna cikin bikin domin gwamnati bata tafiya daidai sai ta samu goyon bayan sarakuna iyayen kasa.

Sarkin Kano Muhammad Sanusi II shi ne shugaban kwamitin shirya bukukuwan. Ya kuma ce yana yin aikinsa ne a matsayinsa na sarkin yakin sarkin musulmi. Yace sarkin musulmi baya son ma a yi bikin amma su ne suke godiya domin irin shugabancin da Allah ya basu. Suna godewa Allah da ya basu shugabanci irin na sarkin musulmi. Suna rokon Allaha ya cigaba da jagorancin. Sarkin Kano yace yana jaddada muba'ayarsa ga sarkin musulmi.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

XS
SM
MD
LG