Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Addinin dake Koyas da Tashin Hankali - Ibrahim Jega


Mai Martaba Sarkin Muslmi Muhammadu Saad Abubakar III, shugaban Musulman Najeriya
Mai Martaba Sarkin Muslmi Muhammadu Saad Abubakar III, shugaban Musulman Najeriya

A zamanin mulkin Samuel Doe a kasar Liberia shugabannin musulunci da na kiristanci sun yi maci zuwa ofishin jakadancin Amurka inda suka bukaci a ware addini da harkokin mulkin gwamnatin kasar da kuma fitinar Charles Taylor.

Wakili daga Liberia Musa Bamba shi yayi wannan jawabin a taron tattaunawa na mabiya addinan duniya da aka gudanar a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Bamba yace wannan matakin da suka dauka shi ya sa Liberia ta zama kasa ta farko da ta yada tattaunawa tsakanin addinai a wata hanyar samun zaman lafiya mai dorewa a Afirka. Wannan ne ma ya kai ga kafa rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar da aka sani da suna ECOMOG.

Bamba ya nuna damuwa inda yace 'yan siyasa da zara sun yi anfani da malaman addini hakonsu kuma ya cimma ruwa, sai suyi watsi dasu a mayarda malaman gugar yasa.

Ibrahim Jega sakataren taron ya nanata manufar addini adalci ne da zaman lafiya. Yace amma ana shiga cikin addini ana aikata aika-aika. Sau tari manufar ita ce cimma wata bukata ta mukamin siyasa ko kuma arzikin duniya. Saboda haka suke tattaunawa tsakaninsu. Sun gano cewa manufofin addinin kirista shi ne tsare gaskiya da mutunta makwafci kuma duk suna cikin addinin musulunci. Yace muddin mutum zai zauna bisa addini ne to babu dalilin kutuntawa makwafci.

A wani gefen kuma Shaikh Yakubu Hassan Katsina yace babu inda addini ya amince da daukar doka a hannu. Yana mayarda martani ne kan zargin da wasu su keyi na mara baya ga gwamna El-Rufai na jihar Kaduna kan soke ayyukan Shiya wai shi ne ya rura wutar rikici. Yace su 'yan IZALA basu taba zama su bada shawarar a kaiwa wani hari ba a koina.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG