Da misalin karfe biyun rana jiya Litinin 'yan kwamitin a karkashin shugabancin Mr. Buba Kaigama suka mikawa kakakin majalisar dokokin jihar rahotonsu.
Sun kai rahoton nasu ne cikin tsauraran matakan tsaro da rakiyar wasu sojoji dake rike da bindigogi. 'Yan kwamitin su bakwai suka je majalisar jihar. Da yake mika rahoton shugaban kwamitin yace sun bi ka'idodin da aka shimfida masu wajen gudanar da aikin.
Kakakin majalisar Ahmed Sintiri wanda ya karbi rahoton ya godewa 'yan kwamitin da aikin da suka yi da basu tabbacin cewa 'yan majalisar zasu duba rahoton su yi nazari da muhawara a kai a lokacin da ya dace.
Bayan karbar rahoton majalisar bata yi wani zama ba yayin da 'yan majalisar suka fice.
Kawo yanzu ba'a san abun da rahoton ya kunsa ba. To saidai wasu sun ce kwamitin ya wanke daya daga cikin mutanen da ake zargi. Ba'a san wanda aka wanken ba, gwamna ko mataimakinsa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5