Kwamitin mutane bakwai da mukaddashin akalin alkalan jihar ya kafa ya fara zama domin jin bahasi game da tuhumar da 'yan majalisar jihar su ke yiwa gwamnan jihar Murtala Nyako da mataimakinsa Bala John Ngilari.
Tun farko babban magatakardan kotunan jihar Alhaji Abubakar M Bayola ya bayyana wa manema labarai cewa bisa doka ba dole ne sai mukaddashin alkalin alkalan ya rantsar da 'yan kwamitin ba. Haka ma Lauya Sunday Wutiri yayi karin haske. Yace abun da ya fi mahimmanci shi ne kafa kwamitin ba wai rantsar da mutanen ba. Bisa ga doka daga ranar da aka kafa kwamitin suna da kwana casa'in su kammala aikinsu.
Magoya bayan gwamnan irin su Baffa Waziri tuni suka fara mayar da martani. Yace a ra'ayinsu dimokradiyar Najeriya ta zo karshe. Sun ji an nada kwamiti to amma suna jira alkali ya rantsar da kwamitin amma ba'a yi ba sai suka ji 'yan kwamitin sun rantsar da kansu. Yin hakan sabawa doka ne. Da sun dauka wadanda aka sa a kwamitin dattabai ne masu kishin kasa amma yanzu sun fahimci cewa kishin kudin da za'a basu suke yi. Matakin ya nuna PDP ta kuduri kawowa jihar masifa ne kawai.
Amma irin su Francis Hamani na ganin matakin da 'yan majalisa suka dauka yayi daidai. Yace dole idan an taka hakin mutum ya tashi. Gwamnan ya taka hakin 'yan majalisa dole ne kuma su nemi hakinsu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5