Kwamitin Binciken Kwangilar Sayen Kayan Tsaro Ya Fara Zama

Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai

Kwamitin binciken kwangilar sayen kayan yaki dake kunshe da manbobi 14 ya samu jagorancinAir Vice Marshall John Ode

Kwamitin ya fara zamansa cikin wannan mako ne a Abuja fadar gwamnatin Najeriya bayan da ya kwashe kwanaki da dama yana tattara takardun bayanai dangane da kwangilolin da suka shafi tsaro.

Kazalika kwamitin ya yi nazarin alkaluman kudaden da aka ce an kashe saboda tsaro da kuma irin kalamun da suka fito daga bakunan manyan hafsoshin sojin kasar yayinda suke jawabin bankwana da gidan soja.

Dr Bawa Abdullahi Wase kwararre kan harkokin tsaro ya yi tsokaci akan binciken. Yace ya sha fada cewa da an dauki kashi daya kawai cikin kudaden da aka ce ana kashewa wajen sayen kayan yaki da 'yan ta'adan Boko Haram bisa gaskiya da basu kai inda suka kai ba yau.

Kwamitin zai binciki ire iren badakalar da ta shafi kwangilar dalar Amurka miliyan dari hudu da sittin da shida da dubu dari biyar saboda yiwa wasu jiragen yaki guda shida kwaskwarima. Akwai kuma kwangilar nera miliyan dubu dari uku na sayo jiragen ruwa na sintiri guda shida. Haka kuma za'a binciki yadda aka wawure kudin euro miliyan dari biyu. Ana harararan 'yan kwamitin shugaban kasa na wancan lokacin kan samarda tsaro a kan ruwan Najeriya.

Wannan kwamitin zai kuma binciki inda zunzurutun kudin nan har dala biliyan daya da majalisar dattawan Najeriya ta amince a ciwo bashinsu da sunan yaki da Boko Haram.

Babban abun da ya fi daure kan masana harkokin tsaro shi ne yadda aka bada kwagilolin ba tare da sanin ma'aikatar tsaron kasar ba.

Ma'aikatar tace abun ya shafi mai baiwa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro ne da kuma manyan hafsoshin sojin kasar kawai. Su ne suka yi ruwa da tsaki a kwangilolin.

Dr Bawa Abdullahi Wase yace babu yadda za'a ce ga ma'aikatar tsaro wadda ita ce take da hakin komi na tsaro wasu sun barta cikin duhu sun sha gaban kansu saboda almundahana domin kasa ta shiga irin halin da ta shiga.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamitin Binciken Kwangilar Sayen Kayan Tsaro Ya Soma Zama