Kawo yanzu kwamitin ya zaga kananan hukumomi guda biyar a jihar Borno inda suka tallafawa mata dari ukku a kowace karamar hukuma da kayan abinci da wasu kayan da ake bukatansu yau da kullum da ake anfani dasu a gida.
A arewacin Borno sun tallafawa matan da suka koma gidajensu wadanda a can baya rikicin Boko Haram ya tilasta masu ficewa daga garuruwansu..
Onarebul Zuwaira Gambo ita ce sakatariyar kwamitin, tace ganin yadda mutane suka fara komawa garuruwansu ya sa matar shugaban kasa Aisha Buhari tace ya kamata a bisu kauyukansu, a taimaka masu domin a kara masu karfin gwuiwa da kuzari. Ta haka ana tallafa masu da kayan abinci da na masarufi.
Kananan hukumomin da aka riga aka rabawa kayan sun hada da Gwozah da Askira Uba da Mafa da Dikwa da Magumeri. A kowace karamar hukuma sun kira mata sun basu kayan da sanin cewa ba su kadai zasu ci abincin ba saboda suna da yara kuma yawancinsu basu da mazaje Boko Haram ta kashesu. Duk karamar hukumar da mutane suka koma zasu bi su da kayan.
Matan da suka karbi tallafin sun yi godiya musamman marayu da yawa marayu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5