Kwallon Kwando: D’Tigress Ta Shiga Jerin Kwararrun Kungiyoyi 10 Na Duniya

'Yan wasan kungiyar kwallon kwando ta Najeriya, D' Tigress (Hoto: Facebook/D' Tigress)

A ranar Alhamis hukumar ta FIBA ta fitar da jerin sunayen kasashen.

Kungiyar Kwallon Kwando ta Mata ta Najeriya, D’Tigress, ta hau matsayi na takwas a jerin ƙasashe na duniya bayan rawar da ta taka a Gasar wasannin Olympics na 2024 a Paris a cewar hukumar kwallon kwando ta duniya FIBA.

A ranar Alhamis FIBA ta fitar da jerin sunayen kasashen.

Wannan karin matsayi ya tabbatar da matsayinsu a cikin manyan ƙungiyoyi goma na duniya, wanda ya sa suka zama ƙungiyar Afirka ta farko—maza ko mata—da ta kai wannan matsayi a jerin kasashe na duniya na FIBA.

Kungiyar ta D’Tigress, it ace ta farko a nahiyar Afirka da ta taba kai wa zagayen quarter-finals a wasannin na Olympics.

Ga jerin kasashen kamar yadda FIBA ta wallafa a shafinta na Facebook: