Mutanen na tsokaci ne kan kuskuren da jirgin sama na soji ya yi, wanda ya hallaka gomman mutane a jihar Kaduna.
Ba da jimawa ba ne rundunar sojin Najeriya ta bakin kwamandan shirin Hadarin Daji da ke gudana a arewa maso yammacin Najeriya Manjo Janar Godwin Mutkut, wadda ta yi magana da yawun babban hafsan mayakan kasa, ta ce ta karbi kayan aiki na zamani don kara matsa kaimi ga yakar ayyukan ta'addanci.
Rundunar sojin dai ta na ci gaba da fafatawa da 'yan ta'adda, kuma duk da yake wasu lokuta ta na samun galaba, da yawa al'ummomi na ci gaba da kokawa kan rashin tsaro.
Hakan ne ya sa kuskuren da jirgin saman soji ya yi a Kaduna, inda ya hallaka mutanen wani gari masu tarin yawa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin al'ummomi musamman mazauna yankunan da rashin tsaro ya yi ka-ka-gida.
Qassimu Abdullahi Isa, mazaunin karamar hukumar Isa ne ta jihar Sakkwato, yankin da jama'a suka jima suna kokawa akan rashin tsaro.
Yace sun yi mamakin jin cewa Najeriya ta na da jirgin yaki da kan iya kashe mutane masu yawa kamar yadda ya faru a Igabi ta jihar Kaduna, amma ta kyale sauran yankunan da ke da matsala suna shan ukubar 'yan bindga. Ya yi kira da a tura musu irin wannan jirgin ya kashe musu barayin dajin da ke addabar su.
Wani mai bibiyar lamurran tsaro a Najeriya kuma dan asalin yankin gabashin Sakkwato, Bashir Altine Guyawa, shugaban rundunar adalci ta Najeriya, yana ganin akwai rashin kwarewa ga aikin wasu jami'an tsaro in har ba su iya bambancewa tsakanin 'yan bindiga da mutanen gari.
Masana lamurran tsaro a Najeriya kamar Dokta Yahuza Ahmad Getso na cewa abin da ya faru a Kaduna, abu ne da ke kara nuna yadda lamarin rashin tsaro ke kara tabarbarewa.
'Yan Najeirya dai na ci gaba da nuna alhini kan abin da ya faru a Kaduna, tare da nuna fatan su na kayan aikin da sojin suka samu su kara taimakawa wajen samar da tsaro a ko'ina cikin fadin kasar.
Your browser doesn’t support HTML5