Kungiyoyin Yan Ta'adda Sun Addabi Kasar Mozambique

Masana sun ce masu ikon fada a ji a kudancin Afrika na da gagarumar rawa da zasu taka a Mozambique domin dakile ayyukan ta’addanci na mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda dake arewacin kasar.

An tattauna batun tashin hankali na Mozambique a makon jiya a taron shugabannin kudancin Afrika da aka gudanar ta yanar gizo, a karkashin kungiyar da ta hada kan kasashe 16, SADC mai hankoron ganin ci gaban kudancin Afrika, ta fannonin siyasa da tattalin arziki da harkar tsaro a tsakanin kasashen.

Taron na zuwa ne yan kwanaki bayan da mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda dake da alaka da ISIS suka kame wata muhimmiyar tashar jirgin ruwa da ke lardin Cabo Delgado, inda ake fama da tashin hankali.

A lokacin taron, shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ya dare kujerar shugabancin nahiyar, wanda masana suka bayyana a matsayin dama da zai iya amfani da ita wajen magance matsalar Cabo Delgado.