Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitocin Kenya Sun Tsunduma Yajin Aiki


Wasu likitocin Kenya yayın sata zanga-zanga a shekarar 2016
Wasu likitocin Kenya yayın sata zanga-zanga a shekarar 2016

Rahotannin na cewa likitoci a yawancin asibitocin gwamnati da ke Nairobi, babban birnin Kenya sun fara yajin aiki domin rashin wadataccen albashi da kayan karıya yayin da suke kula da masu cutar COVID-19.

A cewar sakatare janar na kungiyar likitocin Kenya, Thuranira Kaugiria sun fara yajin aikin ne karfe 12 na dare a yau Juma'a.

Ya ce likitoci 320 wadanda gwamnatin birnin Nairobi ta dauka aiki ne suka fara yajin aikin saboda dumbin matsalolin da suke fama da wadanda suka hada da rashin kayayyakin kariya da kuma rashin wuraren kebe masu cutar COVID-19.

Yajin aikin ba zai shafi asibitoci masu zaman kansu da kuma wadanda ke karkashin gwamnatin tarayya ta kasar ba.

Hoton zanga-zangar wasu likitoci a Kenya
Hoton zanga-zangar wasu likitoci a Kenya

Dama dai likitoci a Kenya sun yi ta wallafa hotuna a shafukansu na Twitter domin nuna irin kayayyakin da ake ba su domin kare kai wadanda suka kira marasa inganci.

Alkaluman baya-bayan nan dai sun nuna cewa akalla mutum 31,441 ne ke dauke da cutar a kasar yayin da mutum 532 suka mutu sakamakon cutar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG