Kungiyoyin SERAP Da CISLAC Sun Maida Martani Kan Sabon Harajin Tsaron Intanet

SERAP

Wasu matakai da gwamnatin Najeriya ke dauka a baya bayan nan zasu kara kuntata wa talakawa, musamman a yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziki, a cewar shugaban kungiyar CISLAC.

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da “ya gaggauta” umurtar Babban Bankin Najeriya (CBN) akan ya janye tsarin cire kudi kashi 0.5 cikin 100 akan kudin da aka tura ta asusun banki a Najeriya, da za a yi amfani da su wajen tabbatar da tsaron yanar gizo, saboda matakin ya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma hakkokin ‘yan kasa a cewar wata sanarwa da kungiyar ta fidda a shafinta na yanar gizo.

Kungiyar ta SERAP ta ce, “Ya zama wajibi gwamnatin Tinubu ta janye wannan umurni da bankin CBN ya sanar cikin sa’o’i 48 saboda ya saba wa doka.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso (Hoto: Facebook/CBN)

Sanarwar ta ce idan ba a janye umarnin cikin sa’o’i 48 ba, kungiyar za ta garzaya kotu.

Da yake maida martani akan batun, Malam Auwal Musa Rafsanjani, shugaban kungiyar CISLAC, mai sa ido kan ayyukan Majalisar Dokoki a Najeriya, ya ce umurnin na CBN zai kara takura wa ‘yan Najeriya musamman marasa karfi da masu matsaikacin karfi, sannan zai yi wuya ‘yan Najeriya su ba da gudummuwarsu wajen habbaka tattalin arzikin kasar idan suna cikin matsatsi.

Auwal Musa Rafsanjani

Bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a shekarar da ta gabata, da nufin kyautata rayuwar talakawa, har yanzu talakawan basu gani a kasa ba, a cewar Rafsanjani.

A kwanan nan kuma hukumar kula da lantarki ta kasa ta bijiro da matakin yin karin kudin wutar lantarki duk da cewa babu ingantacciyar wuta a sassan kasar da yawa.

Rafsanjani ya kara da cewa matakan da gwamnati ke dauka ba sa taimaka wa jama’a sai dai ma su kuntata musu, shi ya sa yanzu wasu ba sa kai kudadensu banki.

Saurari hira da Auwal Musa Rafsanjani:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin SERAP Da CISLAC Sun Maida Martani Kan Sabon Harajin Bankin CBN