Kungiyoyin Rajin Shugabanci Nagari Sun Yi Taron Fadakar Da ‘Yan Takarar Gwamna A Jihar Kano

Kungiyoyin Rajin Shugabanci A Najeriya Sun Yi Taron Fadakar Da ‘Yan Takarar Gwamnan Jihar Kano

An yi kira ga 'yan takarar da su rika sanya ido akan wadanda suka nada a mukamai domin su tabbatar da cewa sun rike amana.

KANO, NIGERIA - A ci gaba da tunkarar babban zabe a Najeriya, kungiyoyin rajin shugabanci na gari a kasar sun shirya taron fadakar da 'yan takarar gwamnan Kano kan mahangar addinin musulinci a shugabanci da jagorancin Jama'a, inda aka fayyace matsayin amana da girman alkawari.

A yayin taron na musamman wadda ya kunshi matasa da dattawa mata da maza da kuma kwararru a fannoni daban daban na rayuwa, shehunnan malamai sun gabatar da bayanai masu zurfi kan batutuwan da suka shafi shugabanci a musulinci da kuma nunawa ‘yan takarar nauyin dake tattare da shugabancin al’uma.

Kungiyoyin Rajin Shugabanci A Najeriya Sun Yi Taron Fadakar Da ‘Yan Takarar Gwamnan Jihar Kano

Sheikh Muhammad Nur Khalid Daraktan cibiyar bincike da harkokin da’awa da ke Abuja, ya ce bai kamata shugabanin su dinga amincewa da mutanen da suke nadawa a kujerun mulki ba, la’akari da yadda dabi’ar bil’adama ke sauyawa a konawane lokaci.

A cewar shi, hakan ta sanya tilas ne shugabannin su rinka sanya ido akan wadanda suka nada domin su tabbatar da cewa, suna rike da amana kamar yadda ya kamata.

Kungiyoyin Rajin Shugabanci A Najeriya Sun Yi Taron Fadakar Da ‘Yan Takarar Gwamnan Jihar Kano

Comrade Kabiru Sa;idu Dakata, daraktan kungiyar CAJA mai rajin shugabanci na gari da tabbatar da dai-daito da kuma amanar Jama’a ya ce makasudun taron shie samar da wani sabon salo na hada ‘yan takara da al’umar gari domin ji daga malamai, wadanda ake yiwa lakabi da magada Annabawa, musamman la’akari da cewa, kusan kashi dari bisa dari na al’umar jihar Kano musulmi ne.

‘Yan takarar Jam’iyyun PRP da LP da kuma NNPP, wato Salihu Tanko Yakasai da Engr Bashir I. Bahshir da kuma Abba Kabir Yusuf ne suka halarci taron kuma sun tabbatar da cewa, sun ji abubuwa da dama daga malaman da suka gabatar da nasiha da tanbihi akan nauyin shugabanci, suna masu alkawarin aiki da abin da suka ji bayan sun samu nasara a zabe.

Kungiyoyin Rajin Shugabanci A Najeriya Sun Yi Taron Fadakar Da ‘Yan Takarar Gwamnan Jihar Kano

A yayin ganawar, mahalarta taron sunyi tambayoyi ga ‘yan takarar da ma neman Karin haske daga malaman da sukayi lacca da nasiha, baya ga nanata muhimmancin baiwa kamfanonin gida kwangilar gwamnati domin yaki da fatara da kuma samar da yanayi mai kyau ga makomar rayuwar mata da yara da sauran al’amuran kyautata rayuwar al’uma.

Sauarari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Rajin Shugabanci A Najeriya Sun Yi Taron Fadakar Da ‘Yan Takarar Gwamnan Jihar Kano.mp3