ADAMAWA, NIGERIA - A hukuncin, wanda aka yanke ranar Jumma'a, kotun, bisa jagorancin Mai Shari'a A.M. Anka ta ce zaben bai bisa ka'ida, saboda haka Senata Aishatu Dahiru Ahmed Binani ta daina gabatar da kanta a matsayin 'yar takarar gwamnan jahar Adamawa ta jam'iyyar APC.
Idan an tuna dai, mutumin da ya kara da Senata Aisha Binani a zaben na fidda da dan takara, wato tsohon shugaban Hukumar Yaki Da Laifukan Da Su Ka Shafi Kudi da Yin Zagom Kasa Ga Tattalin Arziki, Nuhu Ribadu, ya ruga kotu, inda ya bukaci a rusa zaben, wanda aka gudanar ranar 27 ga watan bayan da Senata Aisha ta yi nasara.
Comfort Ibrahim Ezira shugabar kungiyar mata ‘yan siyasa a Jihar Adamawa, wadda kuma ita ce ta jagoranci zanga-zangar, ta bayyana cewa su mata suna bukatar adalci akan wannan shari'a da babbar kotun gwamnatin tarayyar Nigeria ta yanke.
Madam Duni Musa Jambutu kuwa ta ce ta wakilci mata ‘yan kasuwa a wannan zanga-zanga domin ba su ji dadin wannan al’amari ba. Ta na mai bayyana cewa an nuna ma mata bambancin jinsi da kuma danniya a siyasance.
Ita ma Senata Aishatu Dahiru Amed Binani ta yi kira ga Al’ummar Jihar Adamawa da su yi hakuri da abin da ya faru, kuma za su yi dukkan mai yiuwa domin ganin al’amarin ya daidaita.
Shi kuwa Mustafa Salihu Mataimakin Shugaban jam’iyyar ta APC Shiyarar Arewa Maso Gabashin Najeriya ya ce a bangaren jam’iyyar ba za su bar al’amarin ya tafi a haka ba suna kokarin daidaitawa,
Saurari cikakken rahoton daga Lado Salisu Muhammad Garba:
Your browser doesn’t support HTML5