NIAMEY, NIGER - Kungiyoyin kwadagon kasar sun yi watsi da batun da suka kira yunkurin jefa talakawa cikin kuncin rayuwa a wani lokacin da can dama ake fama da tsadar ababen masarufi sanadiyyar annobar Coronavirus da illolin mamayar Rasha a Ukraine. Saboda haka suka bukaci gwamnatin ta gaggauta canza matsayi tun wuri bai kure ba.
A yayin taron da ya hada dukkan manyan shugabanin kungiyoyin ma’aikatan kwadago mambobin gamayyar ITN wadanda suka hada da CNT da USTN da USPT da CGSL Nijar, sun ce babu kamshin gaskiya a game da hujjar da gwamnatin kasar ta bayar wajen karin farashin man Diezel, wanda ya tashi daga dari da dala bakwai da tamma guda (538f cfa) zuwa dala dari da talatin da uku da tamma uku (668 f cfa).
Suna masu cewa ba zasu laminci wannan mataki ba kamar yadda muka samu karin bayani daga bakin Sakataren Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta CNT, Mounkaila Halidou.
Tuni aka fara ganin illolin wannan mataki a kasuwanni, inda wasu kamfanonin cikin gida suka fara tsawwala farashi a wani lokacin da akasarin kayan abinci da ake amfani da su a Nijar kan shigo kasar ne daga waje. Abinda kungiyoyin kwadagon ke ganinsa a matsayin wata manuniyar matsalolin da tsadar man fetur ka iya haddasa wa a nan gaba.
Sakamakon lura da dukkan wadanan abubuwa ya sa kawancen kungiyoyin kwadago na ITN gargadin mahukuntan Nijar, su gaggauta janye matakin karin farashin gazoil man dizel a cewar sakataren haddddiyar kungiyar kwadago ta USPT, Kemou Yahaya.
A daren Lahadin da ta gabata ne Ministan kasuwanci Alkache Alhada ya bada sanarwar karin dala asharin da shida na cfa (130 f cfa) akan kowane litar man dizel wanda ke fara aiki daga ranar 1 ga watan nan na Agustar 2022, saboda dalilai masu nasaba da yakin Rasha a Ukraine wanda ya yi sanadin mamayar motocin kasashe makwafta a gidajen man Nijar, inji shi.
Sai dai kungiyoyin sun ce sam ba su gamsu da wadannan hujjoji ba dalili kenan da suka kudiri aniyar kalubalantar gwamnati ta hanyoyin da kundin tsarin mulki ya yi tanadi.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5