Najeriya: Kungiyar Kwadago Ta ULC Za Ta Tafi Jajin Aiki Ranar Litinin

Sakataren Tsare-tsare Na Kungiyar Kwadago Komared Nasir kabir

Kungiyar kwadago ta ULC, kishiyar NLC, za ta fada yajin aiki daga ranar Litinin 18 ga watan nan, idan ba wata yarjejeniya da aka cimma akan bukatun da tace ta gabatarwa gwamnati tun cikin watannin baya ba.

Cikin kungiyoyi dake karkashin ta harda NUPENG, masu dakon man fetur, da ma'aikatan wutar lantarki da bankuna da kuma matuka jiragen sama da na kasa da dai sauranasu.

Sakataren tsare tsare na kungiyar Komared Nasir Kabir, wanda ya bayyana haka a wata hira da yayi da Muryar Amurka, ya ce kadan daga cikin matsalolin su harda Ministar Kwadago Dr. Ngige, wanda yace yana nuna son zuciya, ta wajen fifita kungiyar NLC, domin ya ki ya saki lasisin rijistar kungiyar ta ULC, da kuma rashin biyan ma'aikata albashinsu da gwamnonin jihohi suke yi.

Sahabo Imam Aliyu da Komared Nasir kabir

Da yake sharhi kan illar yajin aikin ga tattalin arziki, shugaban sashen koyon ilmin tattalin arziki da dabarun kasuwanci a kwalejin kimiyya da Fasaha ta jahar Kano, Dr. Lawal Habeeb Yahya, yace hakan zai sake maida hanun agogo baya, ga tattalin arzikin da yake kokarin tsamo kan shi daga koma bayan da ya shiga, shekaru biyu da suka wuce.

Duk kokarin da Muryar Amurka ta yi domin jin matsayar ma'aikatar kwadago abin ya ci tura.

Domin karin Saurari cikakken rahotan Sahabo Imam Aliyu.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Kungiyoyin Kwadago Na ULC Da NLC Zasu Tafi Jajin Aiki Ranar Litinin - 3'04"