Fargabar daukan fansa ta sa shugabanni a duk arwacin Najeriya na ta kiran al'umma kada a dauki matakin fansa a rewacin kasar.
Kungiyar Musulmin Najeriya ta Jama'atul Nasril Islam, JNI, na cewa ya zama wajibi a kira al'umma kada wanda ya dauki fansa.
Sakataren kungiyar ta JNI Dr Kari Aliyu Abubakar shi ya yiwa manema labarai karin haske. Yana mai cewa a matsayinsu na shugabannin addimi suna kira a kai hankali nesa. Sun yi anfani da masallatai sun kira a yi huduba kan zaman lafiya yau a kwantar da hankulan mutane musamman matasa tunda gwamnati ta ce za ta dauki matakai.
Ita ma kungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya ta ce ta gamsu cewa an fara samun zaman lumana a kudancin kasar. Ta kira doka ta yi aikinta akan duk wadanda suka tada hayaniya.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da cikakken bayani.
Facebook Forum