ABUJA, NIGERIA- Auren wuri ga 'yan mata na daga cikin manyan kalubalen da kasashe masu tasowa ke fuskanta ciki har da Najeriya. Kashi 15.7 na 'yan mata a kasar ke aure kafin su kai shekara 15 kuma kashi 43.4 na da aure kafin su kai shekara 18 idan aka kwatanta da kashi 3.2 na maza, a cewar hukumar UNICEF a shekarar 2020.
Ana danganta abubuwan da ke sanya auren wuri a Najeriya da talauci, al’ada, addini, akida da ma yanayin zamantakewa.
Khadija Iya Abdullahi, shugabar gamayyar kungiyoyin mata a Najeriya wato Women Community in Africa, ta ce auren wuri na kawo babbar matsala saboda idan yaro bai gama samun tarbiya a gidansu ba, ba zai iya tarbiyantar da wani ba. Bayan haka matsalar auren wuri na iya kawo cikas ga ilimi da kuma haifar da rashin sanin ciwon kai daga yaran.
Wani bincike da babban bankin duniya tare da cibiyar bincike ta kasa da kasa game da mata suka taba fitarwa, ya nuna cewa a kowacce rana 'yan mata 41,000 ke aure kafin su kai shekara 18 a duniya, wato jimillar 'yan mata miliyan 15 kenan a duk shekara.
Kawo karshen auren wuri na daga cikin manufofin ci gaba mai dorewa na majalisar dinkin duniya da aka sa a gaba har zuwa shekarar 2030 kuma an yi hasashen kashe triliyoyin dalar Amurka don cimma burin. Riga kafin wannan matsalar ta auren wuri shi ne ba 'ya’ya mata ilimi, kamar yadda Hajiya Hadiza Salisu Ingawa mataimakiyar Darakta a sashin ilimi a babban birnin tarraya ta bayyana.
Masanin tattalin arziki kuma babban dan siyasa a Najeriya Ibrahim Dauda, ya bukaci gwamnati ta fito da wasu karin tsare-tare da za su taimaka wa iyaye musamman na karkara wajen karfafa wa 'ya'yansu mata gwiwar zuwa makaranta, domin talauci na daga cikin manyan kalubalen da ke janyo cikas ga ilimin 'ya'ya mata.
A bangaren gwamnati, Ministar harkokin mata a Najeriya Dame Pauline Tallen, ta ce dokokin kare hakkin yara basu bada dama a aurar da 'ya mace ta na kasa da shekara 18 da haihuwa ba, kuma bai kamata a aurar da yarinya da wuri ba tare da ta samu ilimi ba domin yin hakan babban kalubale ne ga kasar.
A halin da ake ciki, adadin yara miliyan 18.5 ne wadanda basa makaranta a Najeriya a cewar hukumar UNICEF kuma kashi 60 daga cikin su yara mata ne.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5