Kungiyoyin Farar Hula Sun Gudanar Da Zanga-Zanga Akan Tsadar Rayuwa A Jihohin Edo Da Osun

Masu Zanga zanga akan tititunan Edo

A ltitinin din nan, mambobin kungiyoyin fafutukar farar hula sun fantsama kan titunan jihohin Edo da Osun akan halin matsin rayuwar da ake fama da shi a Najeriya.

Domin bayyana korafinsu game matsin tattalin arzikin da janye tallafin man ya janyo, kungiyoyin farar hula sun kwarara kan titunan biranen Benin da Osogbo, fadar mulkin jihohin Edo da Osun.

Mambobin kungiyoyin farar hular Edo sun gudanar da zanga-zangar lumana, inda suka bukaci a kawo karshen wahalhalu da yunwa da ake fama dasu a Najeriya a halin yanzu.

A birnin Benin, masu zanga-zangar sun yi tattaki daga dandalin “Kings” zuwa kan titin Akpakpava dauke da kwalaye masu mabambantan rubuce-rubuce irinsu “a kawo karshen matsin tattalin arziki” da “gwamnatin tarayya ki kawo karshen yunwa yanzu” domin bayyana korafe-korafensu.

Dan takarar gwamnan jihar Edo karkashin inuwar jam’iyyar nnpp a zaben dake tafe cikin watan Satumba me zuwa, Dr. Azemhe Azena ya shiga cikin masu zanga-zangar inda ya bukaci gwamnati ta sake nazarin dalilan da suka sabbaba tsadar rayuwar.

Ku Duba Wannan Ma An Gudanar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Ibadan
Ku Duba Wannan Ma Zanga-Zanga Akan Tsadar Rayuwa Ta Sabbaba Rufe Tituna A Birnin Minna

Haka al’amarin ya kasance a Osogbo inda masu zanga-zangar suka hallara a dandalin Nelson Mandela dake tsakiyar birnin, tare da yin kira ga gwamnatin tarayya data kawo karshen matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Masu Zanga zanga akan tittunan Osogbo

Jerin zanga-zangar na ranar litinin na daga cikin wadanda aka gudanar a baya-bayannan akan halin matsin rayuwa a Najeriya.

Ko a makon daya gabata, daruruwan masu zanga-zanga sun hau kan titunan birnin Ibadan dake shiyar Kudu Maso Yammacin Najeriya domin bayyana bacin ransu da salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Gabanin wadannan zangar-zangar, an gudanar da makamantansu a jihar Kano dake Shiyar Arewa Maso Yamma da kuma Neja da ke shiyar Arewa Maso Tsakiyar Najeriya.

Mizanin auna hauhawar farashi ya kai kaso 29 cikin 100 a Najeriya sakamakon janye tallafin man fetur, abinda ya sabbaba tsadar rayuwa a ‘yan watannin baya-bayan nan. Al’amarin dai ya janyo mahawara da zanga-zanga a wasu sassa na kasar.