Kungiyoyin Fafutuka Na Zargin Kwamishinnan Shari’ar Kano Da Jan Kafa Wajen Gurfanar Da Alhassan Ado Doguwa A Gaban Kotu

Alhassan Doguwa

Yayin da al’ummar jihar Kano ke dakon alkawarin da gwamnatin jihar Kano ta yi na cewa, zata gurfanar da shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa wanda aka tuhuma da hannu wajen kisan mutane a yankin mazabarsa, a kwanakin baya, wasu na zargin ta fara gazawa.

Masu fafutikar kare hakkin bil’adama da tabbatar da adalci a Kano su na zargin kwamishinan shari’a kuma Atoni Janar na jihar Kano da jan kafa wajen gabatar da dan majalisa Alhassan Ado Doguwa a gaban kotu.

Tun a makon da ya gabata ne dai kwamishinan shari’ar na Kano, Barrista Musa Abdullahi Lawan, ya shaida wa manema labarai cewa, akwai tuhuma akan Alhassan Ado Doguwa dangane da waccan tarzomar zabe da ta wakana a garin Tudunwadan Dankadai kuma har a kalla mutane uku suka mutu wasu da yawa kuma suka jikkata.

Babbar kotun tarayya da ke Kano ce ta bada belin shi Alhassan Ado Doguwa a Litinin din makon jiya, kwana uku bayan da kotun majistire ta Kano ta mika shi gidan ajiya da gyaran hali gabanin kammala tattara bayanan da suka kamata domin gurfanar dashi a babbar kotun Kano.

Sai dai, masu kare hakkin bil’adama da tabbatar da adalci sun fara zargin kwamishinan shari’ar Kano da laifin jan kafa wajen sake gurfanar da Alhassan Ado Doguwa a gaban sabuwar kotu.

Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata na zauren gamayyar kungiyoyin tabbatar da adalci na Kano, ya ce akwai alamu da suke nuna cewa, shi kwamishinan shari’a na Kano nada sha’awar kare wanda ake zargi, saboda gazawar sa wajen kalubalantar belin da aka bayar na Alhassan Ado Doguwa kuma ya ki gurfanar da shi a gaban kotun data kamata sama da mako guda kenan.

Shi ma a nasa bangaren, tsohon jami’i a kwamitin dakile yaduwar kananan makamai a Afrika ta Yamma, Kwamared Yahaya Shu’aibu Ungogo, ya ce halin da ake ciki a yanzu na nufin cewa, babu wani caji akan Alhassan Ado Doguwa, tun da har yanzu ba a sake gabatar da shi a gaban sabuwar kotu ba, la’akari da belin sa da aka bayar.

Ta yuwu hakan ce ta sanya Kwamared Kabiru Dakata ke cewa, muddin gwamnatin Kano, ta ofishin kwamishinan shari’a, suka ci gaba da jan kafa akan wannan batu, to ba su da zabi, illa su gabatar da wannan batu a gaban kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya da ke birnin Haque wato (ICC).

Kwamishinan shari’a na Kano Barista Musa Lawan Abdullahi ya ki cewa uffan lokacin da Muryar Amurka ta ba shi dama ya kare kansa game da wancan zargi na cewa yana kokarin amfani da dabaru na shari’a domin kashe tuhume-tuhume akan Alhassan Ado Doguwa.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Fafutuka Na Zargin Kwamishinnan Shari’ar Kano Da Jan Kafa Kan Gurfanar Da Alhassan Ado Doguwa A Gaban Kotu.mp3