Kungiyoyin Da Ronaldo Ya Bugawa Wasa Ya Ci Kwallaye 700

Cristiano Ronaldo, Manchester United.

Ronaldo ya ci wa Manchester United kwallaye 144, Real Madrid 450, Juventus 101 da Sporting Lisbon - 5

Cristiano Ronaldo ya zura kwallonsa ta 700 a tarhinsa na taka leda yayin da Manchester United ta doke Everton da ci 2-1.

Wasan yana 1-1 a lokacin da Ronaldo ya doka kwallonsa ta wuce mai tsaron ragar Everton Jordan Pickford a minti na 44.

Dan shekara 37, Ronaldo ya shiga wasan ne a matsayin canji, inda aka cire Anthony Martial aka saka shi.

Ga Kason Kowacce Kungiya Da Ronaldo Ya Ci wa Kwallo

Manchester United (a zamansa a kungiyar sau biyu) – 144

Real Madrid – 450

Juventus – 101

Sporting Lisbon - 5

Ba a hada kidayar da kwallayen da ya ci wa kasar ba.

A kwanakin baya, dan wasan na United wanda dan asalin kasar Portugal ne, ya ce ba zai yi ritaya ba bayan gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a watan Nuwamba.