Kungiyoyin Matasa Sun Bukaci Gwamnati Ta Yi Tankade A Ma'aikatun Ta

Korafe-korafe sun kunno kai karara akan halin ko in kula da gwamnatin shugaba Mohammadu Buhari ta ke nunawa, musamman akan batutuwan iri su wa'adin shekaru na yin aiki, ko kuma wa'adin shekarun haihuwa na ma'aikaci da doka ko kundin tsarin mulki ya tanadar.

To sai dai wasu hadiman Buhari na cewa hurumin sa ne sauya ma'aikata a lokacin da ya ga ya dace a bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Wasu matasa a karkashin kungiyar 'Be The Change Initiative' sun fito fili tare da bayyana wasu abubuwa da suka fahimta da suka daura laifi akan gwamnatin shugaba Buhari, da ke nuna cewa matasan sun jima suna kuka akan irin sakaci da kin bin dokokin da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada ta hanyar ba wa kowa hakkin sa, musamman ma matasa da suka sha wahala, kan kokarin kawo wannan gwamnati a baya, inda suka ce babu wani wanda aka tuna da shi ballantana ma a yi tunanin saka masa da irin hakillo da ya rika yi a wanan lokaci na zaben shekara 2015 zuwa shekara 2019.

Wannan shi ya sa shugaban kungiyar 'Be The Change Initiative' Abdulhamid Abdullahi Dankyarko, ya fito fili ya bada kiyasi na wasu ma'aikatu da ya kamata gwamnati ta duba.

Shi ma shugaban kungiyar a kasa a tsare na shugaba Buhari Injiniya Dokat Kailani Mohammed, ya ce matasa su yi hakuri kadan, akwai abin da aka tanadar mu su.

Abin jira a gani shi ne ko za a iya gama wadanan kamfanoni kafin wa'adin mulkin shugaba Buhari ya cika, har a dauki matasan, lokaci ne kadai zai tabbatar da haka.