Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Na Kalubalantar Matakin Saka Su A Jerin Masu Biyan Haraji

Wasu kayayyakin tallafi da Wata kungiya mai zaman kanta ta kai Gwoza na cihar Borno

Biyo bayan shirin gwamnatin Najeriya na bukatar kungiyoyi masu zaman kansu su rika biyan haraji, ma'abota kungiyoyin sun samu rarrabuwar kawuna, wasu sun amince wasu kuwa sun ce ba kungiyoyin da ke neman riba ba ne.

Bukatar biyan haraji daga kungiyoyi masu zaman kansu na fitowa ne daga hukumar Tara kudin haraji don fadada hanyoyin tara kudin shiga a Najeriya.

Hukumar na nazarin cewa kungiyoyin na samun makudan kudade daga ketare da hakan ya sa ya zama da muhimmanci su rika biyan haraji.

Haka nan shugaban daya daga kungiyoyin matasa na kamfen din zaman lafiya a Arewa, Komred Salihu Dantata, ya ce matakin, tamkar neman dakile ayyukan kungiyoyin ne.

Baya ga batun haraji a na zargin wasu kungiyoyi masu zaman kan su musamman na kasashen ketare da tsoma hannu wajen tallafawa kungiyoyin ta'addanci.

Hakan ya fito fili a Borno, inda a ka samu wata kungiya na koyar da dabarun harba bindiga da amfani da bindigar roba.

Domin karin bayani saurari rahotan Saleh Shehu Ashaka:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Na Kalubalantar Matakin Saka Su A Jerin Masu Biyan Haraji - 3'00"