Kungiyoyi Masu Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Sun Yi Tir Da Matakan Gwamnati

A daidai lokacin da Kungiyoyi masu yaki da cin hanci da rashawa suka yi tir da yadda Gwamnatin tarraiyar Najeriya, ke tafiyar hawainiya a matakan yaki da cin hanci, fadar Shugaban kasa ta ce a yi maza a sauke Abdurashid Maina.

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bukaci a gaggauta sauke Abdulrashid Maina, da ake zargin an mayar da shi aiki bayan hukumar EFCC na zargin sa da yin sama da fadi da kudaden Pansho, har na Naira Biliyan Dari Biyu da Saba’in da Biyu.

Malam Bashir Baba, Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya bayyana cewa da sake domin lamarin na nema ya zama tamkar wasan yara, domin a cewarsa akwai wadanda aka zarga da yin sama da fadi da dukiyar al’umma amma har yanzu gwamnati bata aiwatar da komai a kansu ba.

Tuni dai wasu kungiyoyi irinsu Concern Nigerians, suke zaman durshan a dandalin hadin kan kasa a birnin tarayya Aabuja, domin nuna damuwarsu a kan wannan al’amarin.

Shugaban kungiya Mr Deji Adeyunju shine shugaban kungiyar kuma ya bayyana cewa dalilin fitowarsu ita ce domin su bayyana damuwarsu akan irinsu Baba Chir Lawal, kwamitin binciken da aka kafa ya san satar da yayi amma saboda abutar su da shugaba Buhari, har yanzu bai ce komai a kansa ba, da makamantansu. Daga kaske ya jaddada cewa zasu ci gaba da fitowa har sai shugaba Buhari ya dauki mataki akai.

Sai dai ga shugaban kungiyar wayar da kan jama’a ta Najeriya, Garba Abari cewa ya yi kamata ya yi a sa ido aga abinda gwamnati zata yi domin a cewarsa wannan gwamnatin bata da wani shafaffe da mai idan akan maganar cin hanci da rashawa.

Daga Abuja ga rahoton Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyi Masu Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Sun Yi Tir Da Matakan Gwamnati