Kungiyoyi Daban-Daban Na Cigaba Da Allah Wadai Da Kisan Da Aka Yiwa Marigayiya Harira

Harira Jibril.

Kungiyoyi da al'umomi daban-daban na cigaba da Allah wadai da kisan da 'yan-bindiga su ka yiwa Harira mai dauke da juna biyu da 'ya'yan ta hudu a jahar Anambra.

Kisan Harira Jibril mai shekaru 32, da 'ya'yan ta Fatima, Khadija, Aziza da Zaituna dai ya jawo hankalin kungiyoyi daban-daban ciki har da Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN, reshen jihar Kaduna wanda ta ce kisan ya kara tabbatar da tabarbarewar tsaro a Najeriya baki daya.

Shugaban kungiyar Rabaren Joseph John Hayeph ya ce dole 'yan Najeriya su jingine banbancin addini da kabilanci don magance matsalar tsaro.

Harira Jibril

Ita kuwa gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, CNG cewa ta yi nuna halin ko'in-kula na mahukunta ne matsalar wannan kasa, a cewar shugaban kwamitin amintattu na gamayyar, Alh. Nastura Ashir Sheriff.

Matsalar tsaro da kuma kisan gilla ga wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba na cigaba da karuwa a sassan Najeriya, abinda ya sa masu ruwa da tsaki ke jan hankali gwamnati ta gaggauta daukar matakai kafin abun ya gagari kundila.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyi Daban-Daban Na Cigaba Da Allah Wadai Da Kisan Da Aka Yiwa Marigayiya Harira

Harira Jibril