Kungiyar ta sanarda sake kai hari akan rijiyar hakan mai mallakar kamfanin Chevron na kasar Amurka a yankin jihar Delta.
A cikin sanarwar kungiyar tace sojojin Najeriya ba komi ba ne garesu kuma ba zasu iya hanasu kai farmaki ba a kowane lokaci da koina suka ga dama a kan kamfanonin mai dake yankin.
Janar Rabe Abubakar daraktan yada labarai na rundunar sojin Najeriya yace hare haren 'yan tsageran ba zasu hanasu cigaba da shirye-shiryensu ba domin kare kadarorin gwamnati da na mutanen da basa cikin kungiyar tsagerun.
Sojoji zasu cigaba da zakulo duk wadanda suke da hannu a aikata ayyukan ta'adanci sanu a hankali. Yace suna daukan matakan kaucewa farma wadanda basu ji ba basu gani ba.
Ahmed Tijjani Baba Gamawa wani mai sharhi kan tsaro ya yi tsokaci akan lamuran dake faruwa musamman dangane da wannan sabuwar kungiyar Niger Delta Avengers. Yace abubuwan dake faruwa basu da dadi. Yace an yi kokarin baya masu bukatunsu har ma an dauki 'ya'yansu an kaisu karatu kasashen waje amma har yanzu suna tada kayar baya. Yace mutanen ba kasar suke so ba aljihunsu suke cikawa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5