Yankin dai na Ogoni ya gurbace shekara da shekaru sakamakon ayyukan hakan danyan mai da aka sha yi shekaru da dama.
Wanna ziyarar shugaba Muhammad Buhari tana zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kungiyyar tsagerun Niger Delta da suke kiran kansu Niger Delat Avengers ko NDA ke tsananta kai hare-hare ga kamfanonin mai tare da yiwa lafiyar shugaban barazana. To saidai duk bangarorin tsaron kasar sun tsaya tsaf domin ganin ziyarar ta gudana lafiya.
Mai magana da yawun 'yansandan jihar Rivers DSP Ahmed Kidaya Muhammad yace suna shirye kan ziyarar shugaban kasa kuma sun tattauna da duk wadanda ya kamata su tattauna dasu akan ziyarar. Baicin shirin da 'yansandan suka yi akwai kuma goyon bayan sojoji.
Yace abubuwan dake faruwa a jihar Delta basa faruwa a jihar Rivers. Ke nan su basa fuskantar wata barazana daga koina.
An dade ana tafiyar hawainiya akan gyaran muhallin yankin Ogoni. Ko Majalisar Dinkin Duniya ma ta gargadi a gaggauta gyaran muhallin amma sai yanzu da gwamnatin Buhari ta zo ta mayar da hankali kai.
Ga karin bayani.