WASHINGTON, DC —
A jihar Adamawa, jami’an tsaro da kungiyar hadakar Fulani Tabital Fulaku, sun bankado gungun wasu masu satar shanu da mutane, suna amsan kudin fansa.
Alhaji Aliyu Nuhu,wani jigo a kungiyar ta Tabital Fulaku, yace “Lallai mun samu masu satar mutane yanzu haka wadanda muka kama suna wajen C.I.D.an tsaresu a jihar Adamawa.”
An dai samu wannan nasaran ne da taomakon Hassan Ibrahim dan gidan Ali Kwara dake taimakawa jami’an tsaro, yace hadin kai daga jami’an tsaro ya taimaka gaya, yace sun samu bindigogi biyu da albarusai guda dari da ashirin, wadanda aka sacen sun tabbatar cewar su suke sace su.