Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Jihar Filato Yaki ci Yaki cin Yewa


Rundunar tsaro na masamman a jihar Filato, ta tabbatar da samun gawar mutun daya daga cikin mutane shida da aka sace sun daga kauyen Bang, dake karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato.

A cewar kakakin rundunar tsaron a jihar ta Filato, Captain Ikedichi Iweha, rundunar na kan binciken makiyaya Fulani, guda biyar da suka bace a yankin.

Bayanai na nuni da cewa an samu yamutsi tsakanin sojoji da al’umar yankin mararaban Foron, inda aka raunata mutanen ukku.

Kakakin Gwamnatin jihar Filato, Samuel Nanle yace Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaron a jihar, yana mai cewa daga hawan sa kan mulki, Gwamna Simon Lalong, ya fara ganawa da Fulani da kuma kabilar Birom.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Yusuf Adamu Gardi, yace majalisar dokokin jihar ta nada kwamiti da zai bincike musabbabin rikicin da kuma hanyoyin da za’a magance su.

XS
SM
MD
LG