Kungiyar SERAP Ta Maka Gwamnonin Jihohin Najeriya 36 Kotu

SERAP

Ƙungiyar kare ‘yancin ‘yan ƙasa da Bibiyar Ayyuka ta SERAP ta maka Gwamnonin jihohin 36 na Najeriya da Ministan Abuja babbar kotu a jihar Legas bisa zarginsu da gazawa wajen ƙididdigar ayyukan da suka yi da kudaden lamuni da suka karba da ya kai har dalar Amurka biliyan 4.6 da kuma Naira tiriliyan 5.9.

A karar da ta shigar, SERAP na son kotu ta ba wa Gwamnonin umarnin gayyato hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da ICPC, domin su binciki yadda Gwamnoni da Ministan Abuja suka salwantar da kuɗaɗen lamunin da aka ba su.

Kazalika, SERAP ta ce, doka ta ba wa ‘yan Najeriya ‘ƴancin sanin yadda Gwamnoni suka salwantar da kuɗaɗen lamunin da suka ƙarba, tunda da sunansu aka ba su rancen.

Kungiyar dai ta ce a rahoton da ta tattara, na cewa gwamnonin na karkatar da akalar kuɗaɗen lamunin, da kuma wadaƙa da su wajen biyan buƙatunsu.

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi A. Sule, ya ce “manufofin bin diddigin ayyuka da kungiyar SERAP ke yi abu ne mai kyau, sai dai kungiyar na aiwatar da ayyukanta ne, ba bisa yadda ya dace ba, domin kamata ya yi ace kungiyar ta samu masu ilimin da za su gudanar da ire-iren wadannan bincike, ba tare da siyasantar da lamuran ba.

Gwamna Sule, ya ce idan har wannan bin diddigin ayyuka da kungiyar ke yi, domin bata ma wani suna ne, to ba za su samu hadin kan jama’a ba”.

Barrister Haruna Magashi, lauya mai zaman kansa, kuma ya ce “sashi na 308 na kundin tsarin mulkin kasa, ya ba wa shugaban kasa, da mataimakinsa dama gwamnoni da mataimakansu, kariya akan cewa baza’a iya shigar dasu kara kotu ba, idan har suna kan karagar mulki.

Barrister Magashi, ya kara da cewa amma “wannan tanadi na kariya da kundin tsarin mulki ya basu, ba zai hana a shigar da ofisoshinsu kara ba”.

A hirarsa da Muryar Amurka, Dr. Isa Abdullahi Kashere manazarci kuma masanin tattalin arziki a Jami’ar Tarayya dake Kashere Jihar Gombe ya ce “dole kungiyar SERAP ta yi zargin Gwamnoni sun yi wadaƙa da kuɗaɗen lamunin da aka ba su, ganin cewa ansha basu ire-iren wannan kuɗaɗe amma talaka baya gani a ƙasa.

Kungiyar SERAP dai na buƙatar gwamnoni da ministan babban birnin tarayya Abuja, da su gabatar da yadda suke salwantar da biliyoyin kuɗaɗen da ake ba su, domin ta haka ne za a iya magance matsalar cin hanci da rashawa da kuma kauce wa zargi.

Saurari cikakken rahoto daga Ruƙaiya Basha:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar SERAP Ta Maka Karar Gwamnonin Najeriya 36 Zuwa Kotu.mp3