Kungiyar Sa-kan CJTF Ta Sako Daruruwan Yara

Wata kungiyar matasa ‘yan sa-kai da ake kira Civilian Task Force da turanci (CJTF), dake goyon bayan yakin da gwamnatin Nigeria ke yi da mayakan Boko Haram ta sako tarin yaran da aka ce yawansu ya kusa dari tara.

Bayanin da Cibiyar Yara ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta bayar a yau Jumma’a, ya bayyana cewa kungiyar ‘yan bangar ta sako jimillar yara 894 a garin Maiduguri dake arewa-maso-gabascin Nigeria a matsayin “wani mataki na ganin cewa an hana gallazawa yara da kuma saka su a cikin ayyukkan da basu dace da su ba.

A shekarar 2013 ne hadakar kasashen da Amurka ke jagoranta suka kafa kungiyar ta CJTF don taimakawa ta fannin kare al'ummomi daga hare-haren 'yan boko haram a arewa maso gabashin Najeriya. Amma Kungiyar 'yan sa-kan ta dauki daruruwan yara aiki