Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Shugaban Kasar Nijar, Ya Musanta Wani Labari


Ministan cikin gidan Nijar Bazoum Muhammad
Ministan cikin gidan Nijar Bazoum Muhammad

Ministan cikin gida na jamhuriyyar Nijar, ya fara da wanke kansa daga zargin yiwa ayyukan hukumar zabe ta CENI katsalandan. A fannin gudanarda zabe yace ba muda kowace allaka da hukumar zabe ta CENI mai zaman kanta, dama da ana bukatar amshewa gwamanti tsare tsare da gudanarda ayyukan zabe, don haka aka kafa wannan hukumar ta musamman mai kula da zabe.

Ya kara nanata cewa kowa ya tabbatar hukumar tana da 'yancin kanta, kuma a ci gaba da zargi ministan cikin gida da gudanarda zabe, to ya kamata mu san abunda muke so.

Jama'a sun kalubalanci yadda Bazoum Muhammad ya kasance dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya, kuma har ila yau ministan cikin gidan da kuma na duk ayyukan da suka shafi addini a Nijar.

Yace ai ko bai kasance a matsayin ministan cikin gida ba, wani abokin aikina ne zai kasance a wannan mukami, kamar Kalla Moutari ko kuma wani daban, koma na zama firai minista, to ai ya kamata mutane su fara maida hankali akan hakan.

Ban kasance akan wannan mukami, domin kuwa koda wani dan jam'iyyar PNDS Tarayya ne ya kasance akan mukami, to shima za a masa wannan zargin.

Sai dai in suna so su ce muna suna bukatar wata gwamanti daban, ta 'yan baruwan mu, mutane su ta yin abubuwan da suke so, to fa ba zamu amince da hakan ba, dokar kasa baki daya ta haramta hakan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG