Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masarautar Kano Zata Samu Karin Sarakunan Yanka 4


Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi
Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi

Kwana daya bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu akan dokar kirkiro da sabbin masarautu 4 a jihar Kano.

A jiya ne dai gwamnan ya sanya hannu akan daftarin dokar kula da nadi da kuma aikace-aikacen sarakuna a jihar Kano, bayan da majalisar dokokin jihar ta kammala aikin kwaskwarima a gundarin dokar.

Baya ga sauye-sauye da ‘yan majalisar suka gudanar a cikin sassan dokar, wani sashi na ta ya bada dammar kirkiro da masarautu guda hudu karin akan wadda ake da ita wato masarautar Kano.

Sabbin masarautun sun hada masarautar Karaye, Rano, Gaya da kuma Bichi.

Sai dai guda cikin dattawan Kano wanda ya fito daga tsatson Dan bazawa masu rike da sarautar Sarkin Ban Kano, ya yi tsokaci game da wannan al’amarin.

A hannu guda kuma talakawan gari na ci gaba da tofa albarkacin bakin su.

Rahotanni sun inganta cewa, daga yanzu zuwa kowane lokaci, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, zai mika takardar nadi ga sabbin sarakunan guda hudu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG