Kungiyar Red Cross Ta Roki Boko Haram Ta Saki Ma'aikatanta Biyu

Tim PMI terus melakukan upaya evakuasi jenazah di berbagai titik di Sulawesi Tengah. (Foto courtesy: Humas PMI)

Kwamitin ayyukan jinkai na kasa da kasa yana rokon gaggawa ga kungiyar mayakan Najeriya dake mubaya’a da kingiyar IS a Afrika ta Yamma, ta saki ma’aikatan lafiya biyu da tayi garkuwa dasu farkon shekarar nan.

Kwamitin na Red Cross ya ce yanzu ya rage kasa da sa’oi ishiri da hudu wa’adin da aka bayar na kashe daya daya cikin ma’aikatan kiwon lafiyan ya cika.

An sace ma’aikatan jinyan Hauwa Mohammed Liman da Alice Loksha a watan Maris tare da wani ma’aikacin jinya lokacin da suke aiki a garin Rann inda ‘yan gudun hijira suka sami mafaka, wani wuri da mayakan suka kai hare hare a lokutan baya. Harin ya jefa yankin cikin matukar bukatar ayyukan magani.

Kungiyar IS ta kashe Hussaini Ahmed Khorsa daya ma’aikacin jinyar a watan Satumba. Kwamitin na Red Cross yace yana iyaka kokari domin ganin haka bata faru da Liman da kuma Loksha ba.

Gwamnatin Najeriya tace tana ci gaba da kokarin ganin an saki dukan wadanda kungiyar ta sace da suka hada da Leah Sharibu, daliba ‘yar shekaru goma sha biyar da aka sace a makarantar Dapchi a wani yanayi daban cikin watan Fabrairu.