Kungiyar NATO Na da Kwarin Gwiwar Amurka Za Ta Ci Gaba Da Tallafawa Ukraine

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky

Da yake magana da manema labarai kafin fara taron kwanaki biyu na ministocin harkokin wajen kasashen NATO a Brussels ta kasar Belgium, Stoltenberg ya jinjinawa, abin da ya kira namijin kokari na tallafin soji da kawayen kungiyar ta NATO suka baiwa Ukraine.

Sakatare janar na Kungiyar kawancen tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce, ya na da kwarin gwiwar cewa Amurka za ta ci gaba da samar da tallafi ga Ukraine duk da rarrabuwar kai da ake samu tsakanin yan majalisar wakilan kasar game da amincewa da karin tallafin kudi ga Ukraine a yakin da take gwabzawa da Rasha.

Da yake magana da manema labarai kafin fara taron kwanaki biyu na ministocin harkokin wajen kasashen NATO a Brussels ta kasar Belgium, Stoltenberg ya jinjinawa, abin da ya kira namijin kokari na tallafin soji da kawayen kungiyar ta NATO suka baiwa Ukraine, a kokarin mai da martanin da kasar ke yi ga yakin Rasha.

Stoltenberg ya kara da cewa, babban kalubale a yanzu, shi ne na bukatar dorewar irin wannan tallafi.

Ya bayyana cewa tallafawa Ukraine abu ne da ya zama wajibi ga NATO.

Yace samun nasarar Rasha a Ukraine, babban bala’i ne ga Ukraine din, kuma gagarumin hadari ga kasashe manbobin kungiyar NATO.