Kungiyar ta Serie A ta riga ta yi hasarar wasu ’yan wasa da dama a wannan kasuwar musayar 'yan wasa kuma ba za ta sayar da dan wasan gaba na Super Eagles koda a kowane farashi ne.
A farkon kasuwar musayar, Napoli ta baiwa Osimhen dama ya tafi bayan da wasu kungiyoyin Frimiya ta Ingila suka nuna sha'awarsu ga dan wasan.
Sai dai kuma ‘yan Neapoli sun yi fatali da kudin sayen dan wasan mai shekaru 23 na Yuro miliyan 120. Suma ‘yan kasar Italiya ba su samu dan Najeriyab da sauki ba, saboda sun biya babban kudin a tarihin kulob din da kuma Afirka da ya kai Yuro miliyan 81 don karbo shi daga Lille shekaru biyu da suka wuce.
Sai dai Arsenal da Manchester United sun yi tambaya game da Osimhen, babu wata kungiya da ta kai tayin neman matashin. kuma yayin da za a fara gasar wasan Seria A ta 2022-2023 a cikin 'yan kwanaki masu zuwa, Napoli tana dogara kan Osimhen don jagorantar ‘yan wasan gaba cikin watanni 12 masu zuwa.