A cikin sanarwar da ta fitar, wata kungiya a birnin Ikko mai suna “The Muslim Right Concern” ta soki tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo tare da bayyana cewa, ya bar jaki yana dukan taiki. Bisa ga cewar kungiyar, kamata ya yi tsohon shugaban kasar ya dora tsaiko da kuma tafiyar hawainiya da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi a kan ‘yan majalisar tarayya wadanda kungiyar tace suna watsi da duk wani shirin gina kasa da shugaba Muhammadu Buhari ke gabatar masu.
Shugaban kungiyar Professa Ishak Akintola yace kungiyarsu bata goyon bayan wannan matsayi na Dr Olusegun Obasanjo, kuma tana kira gareshi da ya janye wannan wasika da ya rubuta, tare da yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da wannan wasika. Ya kuma tsaya takarar neman shugabanci a zaben da za’a a gudanar a shekara ta dubu biyu da goma sha tara.
Yace, “A ganinmu shugaba Muhammadu Buhari ya taka rawar gani in banda tarko da ‘yan majalisa ke kafa masa da tuni ya wuce nan, don haka akwai bukatar Buhari ya yi tazarce, domin kuwa sai ya sake dawowa ne zai sami ‘yan majalisa na kwarai da zasu taimaka masa wajen tafiyar da kasa kamar yadda ‘yan Najeriya ke fata.”
Akasarin magoya bayan Muhammadu Buhari da Sashen Hausa ya zanta da su a birnin Ikko, sun dora laifin gazawar Muhammadu Buhari kan ‘yan majalisun tarayya da na dattijai, da kuma na wakilai, wadanda akasarinsu ‘yan jam’iyar PDP ne suka sauya sheka ana dab da gudanar da zabe, wanda kuma har yanzu ana ganin angulu da kan zabo ne suka yiwa jam’iyar ta APC.
Wani mai sharhi kan lamura, Alhaji Ado Dansudu ya bayyana cewa, ko ba komi, shugaba Muhammadu Buhari ya tsufa saboda haka kamata ya yi ya zama uban kasa ya koma gefe ya sa ido, inda yaga ana bukatar gyara yace a gyara.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Babangida Jibril ya aiko mana daga Ikko.
Your browser doesn’t support HTML5