Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Bayyana Al'kiblarta Akan Siyasar Najeriya

Shugabannin Miyetti Allah Kautal Hore.

A karon farko kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta fito fili karara ta bayyana al'kiblarta game da siyasar Najeriya

Duk da cewa mabiya kungiyar suna shan suka dangane da rikice-rikicen dake daukan hankalin mutane musamman a tsakanin makiyaya da manoma.

Abdullahi Bello Badejo shugaban Miyetti Allah Kautal Hore na kasa yace sun yi taron ne su sanarda duniya cewa sun yi zabe a shekarar 2011 amma bayan zaben sai aka dinga kashe masu mutane. Kawo yanzu babu wanda ya tashi a koina a Najeriya ya tambaya menene ya kawo damuwar. Har yanzu wadanda aka tarwatsasu suna nan cikin wahala. Wasu da suka tsira ana gaya masu cewa sun shiga wahalar da suke ciki ne domin sun ki su yi zabe.

Sabili da haka suna nunawa mutane ga bangaren da suka dauka. Yace suna fada karara cewa Fulani zasu zabi gwamnati mai ci yanzu ta cigaba da ayyukanta.

Jihohin Taraba da Nasarawa sun yi kamarin suna a 'yan kwanakin nan dangane da rikice-rikicen gonaki da iyakoki tsakanin Fulani da manoma lamarin da kan jawo asarar rayuka da dama.

Duk da haka shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore daga wadannan jihohin sun ce suna goyon bayan wannan yunkuri na tsunduma tsundum cikin harkokin siyasa tare da fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali zasu samu.

Sajo Muhammed shugaban Miyetti Allah Kautal Hore na jihar Taraba yace da yaddar Allah zasu zauna lafiya tunda sun roki Allah kuma sun fito domin gwamnati ta san dasu suma su bada goyon bayansu tsakaninsu da Allah. Ta wannan dalilin idan Allah ya yadda zasu samu zaman lafiya.

Shi ma shugaban reshen jihar Nasarawa Alhaji Gidado Idris yace idan an bi a hankali zaman lafiya zai dore a jihar. Yace su ne suke yiwa kansu. Babu wani shugaban da yake cewa a je a yi wani abu. Tunda suka samu suka yi wannan zaman dole zasu koma su tabbatar da alkawuran zaman lafiya da suka dauka da kowace kabila.

Dangane da yadda zasu wayar da kawunan mabiyansu kafin zabe mai zuwa shugaban Miyetti Allah na shiyar arewa ta tsakiya baki daya Alhaji Sani Juli yace zasu nada mata da maza su zama kwamiti dinsu. Su ne zasu dinga shiga rugage suna ganawa da ardodin Fulani. Zasu yi zama dasu. Zasu tattauna su nuna masu abubuwan da ake so saboda idan lokaci yayi a hada kai a tafi tare.

Umar Abdullahi Tata wani dan siyasa daga jihar Katsina yace yunkurin da Fulani suka yi yayi daidai. Ko an ki ko an so ba'a samun mulki sai da siyasa. Mulki kuma shi ne ke rayar da al'umma. Mulki kuma shi ne yake hada al'umma. Yace jihadi ne kuma addini ne shiga siyasa. Yace duk ikon shugaban kasa ba zai iya bashi fili a Katsina ba. Ba zai iya nada kansila ko shgaban karamar hukuma a Katsina ba. Al'ummar jihar ce zata nadasu.

Fulani makiyaya da yawansu ya kai miliyan ashirin da uku a Najeriya na ikirarin taka rawa a siyasar kasar musamman a zaben shekarar 2015 sabani yadda suke a shekarun baya.

Ga rahoton Madina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Bayyana Al'kiblarta Akan Siyasar Najeriya - 3' 58"