Kungiyar Matasan Nijar Ta Shirya Taron Yaki Da Tsatsauran Ra'ayin Addini

Kungiyar Matasan Nijar

Wata kungiyar matasa a jamhuriyar Nijar, tare da hadin guiwar cibiyar raya al’adun Amurka, sun shirya wata mahawarar bainar jama’a da nufin fadakar da matasa illolin dake tattare da tsatsauran ra’ayin addini.

Kungiyar matasa da suka samu guarben karatu kyauta a kasar Amurka a karkashin tsarin da ake kira NIGER USA IVLP Alumni Association ce ta shirya wannan taro a matsayin riga kafin barazanar da matasa ke fuskanta daga tarkon kungiyoyin ta’addanci.

Mahalartan mahawara sun yaba da wannan yunkuri da suke ganin zai ankarar da matasa su yi takatsantsan da dukkan wani tayin dake kama da na masu tayar da hankali.

Ofishin jakadancin Amurka ne ya dauki dawainiyar wannan mahawara wacce za a ci gaba da yada makamantanta a sassan Nijar don karfafa zaman lafiya mai dorewa inji shugaban cibiyar raya al’adun Amurka Mr. John Dow.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Matasan Nijar Ta Shirya Yaki Da Tsatsauran Ra'ayin Addini