Kungiyar Matasan Arewa Ta Bukaci a Canja Kwamandojin Sojojin Najeriya

Shugaban kungiyar Matasan Arewacin Najeriya

Mutane da dama na kira ga shugaban kasar Najeriya da ya canja shugabannin sojojin Najeriya gaba dayansu, inda wasu kuma su ke ganin inganta musu kayan aiki shi ne mafita.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Kungiyar Matasan Arewa ke nuna bacinranta a game da halin tsaro a kasar ba. A shekara 2014 ma dai kungiyar ta nuna bakin cikinta tare da kalubalantar gwamnatin wancan lokacin akan inganta tsaron kasar, sannan ta yi kiran a inganta hukumomin tsaron kasar gaba daya.

Shugaban Kungiyar Isa Abubakar ya ce lokaci ya yi da shugaba Muhammadu Buhari zai canja shugabanin hukumomin tsaron kasar, ya kawo sababbin shugabanin sojojin Kasa, na ruwa da na sama domin su yi amfani da sabbin hanyoyi wajan magance matsalolin tsaron da ake fama da su.

Shi ma shugaban Kungiyar Muryar Talaka a Arewa Maso Gabas, Sale Bakoro Damaturu, ya goyi bayan matakin da matasan suka dauka, har ya kara da cewa Shugaba Mohammadu Buhari ya kamata ya gana da kananan sojojin kasar saboda ya san matsalolinsu domin ayi saurin magance su.

Amma shi kuma Dr. Abubakar Umar Kari kwararre a fanin zamantakewa kuma malami a Jami'ar Abuja yana ganin sauya shugabannin jami'an tsaron ba shine mafita ba.

Ga Medina Dauda da cikkaken Rahotan

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Matasan Arewa Sun Yi Kira Da Canja Shugabannin Sojojin Najeriya