Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buki Ya Rikide Ya Zama Mummunar Tashin Hankali A Bauchi


Shugabannin 'yan sanda Bauchi
Shugabannin 'yan sanda Bauchi

Hukumar ‘yan sanda a jihar Bauchi bada tabbatar da mutuwar wasu matasa guda uku a wajen sharholiyan tunawa da ranar haihuwa da aka gudanar a unguwar Yalwa dake wajen garin Bauchi a daren lahadi kana wasu matasan takwas sun sami raunuka iri dabam dabam a jikinsu.

Tashin hankalin da ya barke a wurin bukin ranar haifuwar, ya yi sanadiyar kona gidaje da mota biyo bayan fada ta kaure tsakanin matasan dake halartan bukin da wani matashi ya shiryawa kansa, lamarin da ‘yan sandan jihar ke ci gaba da bincike akai.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Bauchi, DSP Kamal Datti ya musunta cewa wannan rikici yana da alaka da fadar kabilanci ko ta addini kamar yanda mutane ke yayatawa. Ya kuma ki tabbatar da ko fada ce a kan ‘yan mata, lamarin da yace bincike ne kawai zai tabbatar da gaskiyar maganar.

A tattaunawarsa da wakilinmu na jihar Bauchi, DSP Kamal Datti ya shaida masa cewa an kama mutane 76 bisa tuhumar da ake musu da hannu a cikin hargitsin kuma ana ci gaba da neman sauran masu hannu a wannan rikicin domin a hukunta su.

A cewar rundunar ‘yan sandan tuni an samu kwanciyr hankali wurin, yayin da jami’ansu ke ci gaba da sa ido a kan zaman lafiyar yankin. Hukumar ‘yan sandan jihar Bauchi ta lashi takobin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a wannan tashin hankali.

Ga rahoton da wakilinmu a jihar Bauchi Abdulwahab Mohammed ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Facebook Forum

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Halin da monoman shinkafa a Zabarmari na jihar Borno ke ciki bayan da mayakan Boko Haram suka kashe kinamin hamsin, da ya sa wasu kaura
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shugaba Donald Trump ya ba gwamnatinsa damar tasa keyar bakin haure daga kasar, da kai wasu kurkuku na Guantanamo Bay dake Cuba
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG